Somaliya: Sojojin Gwamnati Sun Kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da Talatin
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34174-somaliya_sojojin_gwamnati_sun_kashe_'yan_ta'adda_fiye_da_talatin
Majiyar gwamnatin kasar ta Somaliya ta tabbatar da cewa an kai wa 'yan kungiyar al-shabab hari ta sama, da ya yi sanadiyyar kashe 37 daga cikinsu.
(last modified 2018-11-21T04:41:40+00:00 )
Nov 21, 2018 04:41 UTC
  • Somaliya: Sojojin Gwamnati Sun Kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da Talatin

Majiyar gwamnatin kasar ta Somaliya ta tabbatar da cewa an kai wa 'yan kungiyar al-shabab hari ta sama, da ya yi sanadiyyar kashe 37 daga cikinsu.

Majiyar ta ce sojojin sun kai hare-haren ne har sau biyu a yankuna daban-daban da 'yan kungiyar ta al-shabab suke da sansanoni.

A gefe daya wata kungiya mai alaka da Da'esh ta ja kunnen al-shabab akan duk wani yunkuri na fada da ita domin za ta fuskanci mayar da martani.

Kungiyar ta ce a yanzu lokaci ne da za su rika daukar fansa akan duk wani wuce gona da iri da kungiyar ta al-shabab za ta aikata.

Kasar Somaliya ta fada cikin rashin tsayayyar gwamnati tun daga 1991, abin da ya haddasa bullar kungiyoyin daban-daban masu dauke da makamai.

Kungiyar al-shabab wacce ta yi wa alka'ida mubaya'a, tana a matsayin barazana ce ga zaman lafiyar kasar da kuma kasashen kakwabta.