Amurka Ta Hallaka Mayakan Shebab 37 A Somaliya
Amurka ta sanar da cewa sojojinta sun kai jerin hare hare biyu kan kan sansanonin mayakan Al-shabab, inda suka kashe 37 daga cikinsu.
Sanarwar da tawagar sojin Amurka a Afrika ta (Africom) ta fitar ta ce harin na farko ya hallaka mayakan na Al'shabab 27, a yayin da harin na biyu ya kashe mayakan 10.
Sanarwar ta kara da cewa an kai hare haren ne tare da amincewar gwamnatin Somaliya, a matakin rage karfin kungiyar ta Al'shabab bayan samun labarin cewa kungiyar na shirya kai hare hare a a yankin.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Amurka ke kai hare hare kan mayakan na Al'shabab, inda ko a tsakiyar watan Oktoba da ya gabata wani hari makamancin wannan ya kashe mayakan na Al'shabab 60.
Baya ga Amurka dai gwamnatin Somaliya na samun taimakon tawagar sojojin kungiyar tarayya AFrika ta (Amisom) a yakin da take da kungiyar ta Alshabab.