Boko Haram Ta Kashe Sojojin Najeriya 43
Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya akalla 43 a hare-haren da suka kai a karshen makon jiya.
Bayanai da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya samuy daga wasu majiyoyin sojin Najeriyar, sun ce an kashe akalla dakaru 43 ciki harda wani babban jami'in soji a kauyen Metele dake kusa da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi data gabata.
labarin ya ci gaba da cewa mayakan na Boko haram sun je kauyen ne cikin wata babbar mota dauke da manyan makamai inda suka farma wa kauyen na Maitele da jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriyar.
Babu dai wani bayyani kan wannan labarin daga rundinar sojin ta Najeriya kawo yanzu.
Dama dai kafin hakan wasu rahotanni sun ce kungiyar ta Boko Haram dake kiran kanta reshen kungiyar (IS), a yammacin Afrika ta zazafa kai hare harenta a baya baya nan, wanda ya soma haddasa zaman dar-dar a wasu sassan kasar a daidai lokacin da aka fara yakin neman manyan zabukan kasar.