Ana Ci gaba Da Samun Tashe-tashen Hankula A Kasar Demokradiyyar Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34186-ana_ci_gaba_da_samun_tashe_tashen_hankula_a_kasar_demokradiyyar_congo
Kamfnin dillancin labarun Faransa ya anmbato cewa har yanzu kungiyar 'yan tawayen Uganda da ke gabacin Demokradiyyar Congo na ci gaba da yi wa mutanen ganin Beni barazana
(last modified 2018-11-22T04:12:44+00:00 )
Nov 22, 2018 04:12 UTC
  • Ana Ci gaba Da Samun Tashe-tashen Hankula A Kasar Demokradiyyar Congo

Kamfnin dillancin labarun Faransa ya anmbato cewa har yanzu kungiyar 'yan tawayen Uganda da ke gabacin Demokradiyyar Congo na ci gaba da yi wa mutanen ganin Beni barazana

A cikin shekaru 4 na bayan nan fiye da fararen hula 700 ne 'yan tawayen su ka kashe mafi yawancinsu manoma mazauna kauyukan da suke nesa

Mazauna garin na Beni da ke gundumar Kivo ta arewa suna yin koke akan yadda gwamnatin kasar ba ta kawo musu wani dauki

Tun daga shekarar 1994 ne 'yan tawayen kasar ta Uganada suna kafa sansanoni a gabacin kasar Demokradiyyar Congo inda su ke kai hare-hare mafi yawanci akan fararen hula

Tare da cewa da akwai dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Demokradiyyar Congo, sai dai duk da haka kungiyoyin 'yan tawaye da ke gabacin kasar na ci gaba da zama babbar barazana ta zaman lafiya