Habasha: An Nada Jagorar 'Yan Adawa A Matsayin Shugabar Hukumar Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34198-habasha_an_nada_jagorar_'yan_adawa_a_matsayin_shugabar_hukumar_zabe
Firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad, ya nada tsohuwar shugabar 'yan adawa a kasar Birtukan Mideksa a matsayin shugabar hukumar zabe ta kasa.
(last modified 2018-11-22T13:08:11+00:00 )
Nov 22, 2018 13:08 UTC
  • Habasha: An Nada Jagorar 'Yan Adawa A Matsayin Shugabar Hukumar Zabe

Firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad, ya nada tsohuwar shugabar 'yan adawa a kasar Birtukan Mideksa a matsayin shugabar hukumar zabe ta kasa.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a ci gaba da gudanar da sauye-sauye na ban mamaki da firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad yake yi, a yau ya nada tsohuwar jarorar 'yan adawa a kasar Birtukan Mideksa amtsayin shugabar hukumar zabe, domin ta jagoranci tsara zabukan da za  a gudanar a kasar a shekara ta 2020.

Birtukan Mideksa ta amince da wannan matsayi da Abi Ahmad ya bata, inda ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda alamun da ta gani daga gare shi kan cewa, ya dauko hanyar yin gyara da kuma hada kan al'ummar kasar da ke a warwatse.

Wannan matsayi da firayi ministan ya baiwa fitacciyar 'yar adawa a kasar kuma babbar lauya, na daya daga cikin nade-nade na ban mamaki da yake gudanarwa  a cikin 'yan kwanakin nan, musamman yadda yake bayar da muhimmanci  wajen baiwa mata mukamai a cikin gwamnatinsa, wanda hakan shi ne karo na farko da aka taba yin haka a cikin tarihin kasar Habasha.