Ana Shirin Kai Shugaban Gabon Zuwa Morocco Domin Neman Magani
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34210-ana_shirin_kai_shugaban_gabon_zuwa_morocco_domin_neman_magani
Hukumomin kasar Gabon sun sanar da cewa, za a kai shugaban kasar Ali Bango zuwa wani asibiti a birnin Ribat na kasar Morocco domin kula da lafiyarsa.
(last modified 2018-11-23T15:51:29+00:00 )
Nov 23, 2018 15:51 UTC
  • Ana Shirin Kai Shugaban Gabon Zuwa Morocco Domin Neman Magani

Hukumomin kasar Gabon sun sanar da cewa, za a kai shugaban kasar Ali Bango zuwa wani asibiti a birnin Ribat na kasar Morocco domin kula da lafiyarsa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Ali Bango dan shekaru 59 da haihuwa, yana fama da rashin lafiya wadda ta kwantar da shi tun daga watan Oktoban da ya gabata.

Tun bayan da ya tafi halartar wani taron tattalin arziki a birnin Riyad na Saudiya a cikin watan Oktoba ba a kara jin duriyarsa ba, inda hankulan al'ummar kasar ta Gabon ya tashi, amma daga bisani majiyoyin fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa an kwantar da shi ne a wani asibitia  birnin Riyad saboda rashin lafiya.

Ali Bango dai ya hau kan kujerar shugabancin kasar Gabon ne tun a cikin shekara ta 2009, bayan da ya gaji mahaifinsa Umar bango, wanda ya mulki kasar tun daga shekara ta 1967 har zuwa 2009.