An Zargi Pira Ministan Kasar Tunisiya Da Kokarin Juyin Mulki
Babban sakataren jam'iyyar Nida'u Tunis mai mulki a kasar ya zargi pira minista Yusuf Shahid da kokarin juyin mulki akan shugaban kasa Muhammad al-Baji Qa'id al-sisy.
Salim Rayahi ya bayyana kwaskwarimar da Yusuf Shahid ya yi wa majalisar ministocin kasar da cewa juyin mulki ne, sannan ya kara da cewa jam'iyyar Ni'da'u Tunis wacce pira ministan ya fito daga cikinta za ta dauki matakan da suka dace.
Wannan dai shi ne karo na biyu da shahid ya yi wa majalisar ministocin kasar kwaskarima.
Daga cikin wadanda sabbin nade-naden na Shahid ya hada da su da akwai wani bayahude da ya bai wa ministan yawon bude ido.
Tun dai al'ummar kasar suka fara gudanar da Zanga-zangar kin amincewa da wannan matakin.
Sababi ya kunno kai a tsakanin pira minista Yusuf Shahid da jam'iyyar Nida'u Tunis da yake wakilta