Demokradiyyar Congo: Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Saboda Barazanar Ta'addanci
Nov 25, 2018 09:22 UTC
Ofishin jakadancin na Amurka ya fitar da wata sanarwa da a ciki ya bayyana dakatar da ayukan ofishin jakadancin na wani lokaci saboda barazanar ta'addanci
Sanarwar ta kunshi cewa; Bayani mai inganci ya tabbatar da yiyuwar afkuwar ayyukan ta'addanci akan cibiyoyin da suke na gwamnatin Amurka"
A dalilin haka ofishin jakadancin na Amurka a Kinshasha ya jingine ayyukansa na wani lokaci, haka nan karamin ofishin jakadancin kasar
Sai dai kawo ya zuwa yanzu gwamnatin kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo ba ta bayyana matsayarta ba akan sanarwar ta ofishin jakadancin Amurkan.