Somalia: Kungiyar Al-shabab Ta kai Hari Kan Wata Cibiyar Addini
Kungiyar Al-shabab mai da'awar jihadia kasar Somalia, ta kaddamar da wani hari a safiyar yau a kan gidan wani malamin addini a garin Jalkayur.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau Litinin wata mota da aka shakare da bama-bamai ta shi a kusa da gidan wani malamin addini mai suna Abdul Waliy, wanda gidansa yake hade da wata cibiyar addini da yake jagoranta a garin Jalkayur da ke tsakiyar kasar Somalia.
Wani mutum da yake makwabtaka da wurin mai suna Farah Nur ya sheda cewa, bayan tayar da motar da take dauke da bama-bamai, 'yan bindiga sun kutsa kai a cikin cibiyar da kuma gidan malamin, inda ake ta jin harbe-harbe.
Kungiyar Al-shabab ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kai wannan hari, amma kungiyar ba ta bayyana alilin kai harin ba, kamar yadda kuma har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ko jikkata sakamakon harin ba.