Togo: 'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34300-togo_'yan_adawa_sun_gudanar_da_gagarumar_zanga_zanga
Dubban 'yan adawa sun gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen birnin Lome fadar mulkin kasar Togo, domin nuna rashin amincewa da gudanar da zaben 'yan majalisa.
(last modified 2018-12-02T01:07:48+00:00 )
Dec 02, 2018 01:07 UTC
  • Togo: 'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga

Dubban 'yan adawa sun gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen birnin Lome fadar mulkin kasar Togo, domin nuna rashin amincewa da gudanar da zaben 'yan majalisa.

Rahotanni sun ce magoya bayan babban kawancen jam'iyyun adawa na kasar ne wanda ya kunshi jam'iyyu 14, su ne suka gudanar da zanga-zangar, inda suke yin kira da a dakatar da gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar da ake shirin yi a cikin wannan wata na Disamba da muke ciki.

'Yan adawar suka ce idan har gwamnati ta yi biris da kiran nasu, to su kuma za su haramta zaben, saboda abin da suka kira shirin yin magudi da gwamnatin take da shi a yayin gudanar da zabukan.

Jam'iyyun adawar suna zargin shugaban kasar ta Togo  Faure Gnassingbe da yin kama karya da sunan dimukradiyya.

Faure Gnassingbe ya dare kan kujerar shugabancin kasar ne tun a 2005, bayan mutuwar mahaifinsa wanda ya mulki kasar har tsawon shekaru 38.