An Tsawaita Dokar Ta Baci A Kasar Tunisiya
Shugaban kasar ta Tunisiya ne ya sanar da tsawaita dokar ta baci da kasar take aiki da ita zuwa karin wata daya anan gaba
A wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ta Tuniya ta fitar a jiya Laraba ya bayyana cewa; An tsawaita dokar ne daga juma'a 7 ga watan nan na Disamba zuwa 5 ga watan Janairu na 2019
Ofishin shugaban kasar ya ce; An dauki wannan matakin ne bayan tattaunawar da aka yi a tsakanin shugaban kasa da Pira minista da kuma shugaban majalisar dokokin kasar
A karon farko kasar ta Tunisiya ta fara aiki ne da dokar ta baci tun daga ranar 24 ga watan Nuwamba na 2015 bayan wani harin ta'addanci da aka kai wa motar safa mai dauke da sojoji.
A wancan harin an kashe mutane 38 da suka hada da 'yan sanda 12.
Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta dauki alhakin kai wancan harin