'Yan Majalisar Sudan Na Kokari Ba Wa Shugaba Bashir Damar Yin Tazarce
Rahotanni daga kasar Sudan na nuni da cewa 'yan majalisar kasar sun goyi bayan wani shiri na yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar da zai ba wa shugaban kasar Umar Hasan al-Bashir damar yin tazarce a kan karagar mulkin kasar.
Yayin da yake sanar da hakan, kakakin majalisar dokokin kasar ta Sudan Ibrahim Ahmed Omar ya ce ya sami wasikar da mafi yawa daga cikin 'yan majalisar suka sanya wa hannu suna goyon bayan yin sauyi cikin kundin tsarin mulkin kasar da zai ba wa shugaba Bashir din damar yin tazarce a kan karagar mulkin kasar.
A bisa kundin tsarin mulkin na yanzu dai, shugaba Al-Bashir wanda ke mulkin kasar ta Sudan tun shekarar 1989 ba shi da damar tsayawa takarar shugabancin kasar bayan wa'adin mulkinsa ya kare a shekara ta 2020, hakan ne ya sanya 'yan majalisar suke son a yi gyaran fuska wa kundin tsarin mulkin da zai ba shi damar sake tsayawa a zabe na gaban.
Kasar Sudan din dai tana fuskantar matsaloli na siyasa da tattalin arziki lamarin da ya sanya gwamnatin ta Bashir fuskantar zanga-zangogi daga 'yan adawa wadanda suke kiransa da ya sauka daga karagar mulkin.