Saiful Islam Ya Gabatar Da Shawarwari Domin kawo Karshen Rikicin Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34362-saiful_islam_ya_gabatar_da_shawarwari_domin_kawo_karshen_rikicin_libya
Saiful Islam Ghaddafi dan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Ghaddafi, ya gabatar da wasu sabbin shawarwari da nufin ganin an kawo karshen dambarwar da kasar ta Liya take ciki.
(last modified 2018-12-07T15:35:19+00:00 )
Dec 07, 2018 15:35 UTC
  • Saiful Islam Ya Gabatar Da Shawarwari Domin kawo Karshen Rikicin Libya

Saiful Islam Ghaddafi dan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Ghaddafi, ya gabatar da wasu sabbin shawarwari da nufin ganin an kawo karshen dambarwar da kasar ta Liya take ciki.

Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Saiful Islam ya aike da wata wasika zuwa ga gwamnatin kasar Rasha, wadda take dauke da mahangarsa kan yadda za a kawo karshen rikicin da kasar Libya ta samu kanta a ciki.

Muhammad Qailushi, daya ne daga cikin fitattun 'yan siyasa  a kasar ta Libya, shi ne kuma manzon Saiful Islam zuwa kasar Rasha, inda ya mika wasikar Saiful Islam ga mahukuntan kasar ta Rasha.

Qailushi ya yi bayanin cewa; wasikar ta Saiful Islam ta kunshi mahangar kan yadda za a kawo karshen rikicin Libya, da hakan ya hada da taimaka ma dukkanin al'ummar Libya da su warware matsalolinsu da kansu, su kafa irin tsarin da suke bukata da kansu ba tare da an yi musu shigar shugula ba.

Sai dai masu adawa da Saiful Islam suna ganin cewa wannnan yunkuri nasa idan ya yi nasar zai mayar da kasar kamar yadda take a lokacin Ghaddafi, inda suke ganin an mayar da su gefe daya a cikin dukkanin harkokin siyasar kasar.