Sojojin Nijeriya Sun Dakile Harin Boko Haram A Jihar Borno
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami nasarar dakile wani kokari na kungiyar Boko Haram na kai hari wasu sansanonin sojojin guda biyu da suke yankin.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar wata majiya sojin ta shaida masa cewa sojojin sun sami nasarar dakile da kuma fatattakan 'yan Boko Haram da suka yi kokari kawo wasu sabbin hare-hare sansanonin soji da ke garin Bama da ke kimanin kilomita 70 daga garin Maiduguri babban birnin jihar Bornon.
Wasu bayanai dai sun bayyana cewar mayakan na Boko Haram sun shigo yankunan ne cikin jerin gwanon motoci dauke da muggan makamai da nufin kai hari sansanin sojojin da ke ganin na Bama, to sai dai bayan gumurzu na sa'oi sojojin sun sami nasarar fatattakan 'yan ta'addan ba tare da sojojin sun rasa wani daga cikin mutanensu ba.
Harin da 'yan Boko Haram din suka kai sansanin sojin da ke garin na Bama yana zuwa ne bayan wani kokari da mayakan Boko Haram din suka yi na kai wani harin daren shekaran jiya Alhamis kan wani sansanin sojin da ke garin Rann, wanda ke kan iyaka da kasar Kamaru, to sai a nan ma dai sojojin sun fatattake su.