Tunisiya: An Yi Zanga-zangar Nuna Kin Jinin 'Yan Sahayoniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34379-tunisiya_an_yi_zanga_zangar_nuna_kin_jinin_'yan_sahayoniya
Daruruwan mutanen kasar ta Tunisiya ne su ka fito Zanga-zanga a jiya asabar a birnin Tunis domin yin tunawa da ranar boren Intifadha na al'ummar Palasdinu
(last modified 2018-12-09T08:55:45+00:00 )
Dec 09, 2018 08:55 UTC
  • Tunisiya: An Yi Zanga-zangar Nuna Kin Jinin 'Yan Sahayoniya

Daruruwan mutanen kasar ta Tunisiya ne su ka fito Zanga-zanga a jiya asabar a birnin Tunis domin yin tunawa da ranar boren Intifadha na al'ummar Palasdinu

Kungiyoyin fararen hula da kuma jam'iyyu masu son kawo sauyi na kasar ta Tunisiya ne su ka gayyaci yin Zanga-zangar ta jiya.

An rika bada taken nuna goyon bayan gwagwarmayar al'ummar Palasdinu tare da yin Allah wadai da mamayar 'yan Sahayoniya, kamar kuma yadda masu Zanga-zangar su ka rika yin kira da a hana duk wata alaka da haramtacciyar kasar ta Yahudawa.

A ranar 8 ga watan Disamba na 1987 ne al'ummar Palasdinu suka fara boren da aka fi sani da Intifadha wanda kuma ya ci gaba har zuwa cikin shekarar 1993 da aka yi yarjejeniyar Oslo

Palasdinawan sun rika amfani da duwatsu akan sojojin Sahayoniya da su ka rika jifarsu da duwatsu.