An Hallaka Yan Bindiga 27 A Yankin Sina Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34416-an_hallaka_yan_bindiga_27_a_yankin_sina_na_kasar_masar
Sojojin kasar Masar sun bada labarin halakar yan ta'adda 27 a yankin Sina daga arewacin na kasar
(last modified 2018-12-12T15:51:31+00:00 )
Dec 12, 2018 15:51 UTC
  • An Hallaka Yan Bindiga 27 A Yankin Sina Na Kasar Masar

Sojojin kasar Masar sun bada labarin halakar yan ta'adda 27 a yankin Sina daga arewacin na kasar

Shafin yanar gizo na jaridar Al-Yaumussabe ya nakalto babban komandan sojojin kasar yana fadar haka a yau Laraba ya kuma kara da cewa sojojin kasar tare da masana ilmin kwance nakiya na sojojin sun kwance nakiyoyi 344 a cikin yan kwanakin da suka gabata a wurare daban daban a yankin.

komandan ya kara da cewa yan ta'adda ne suka dana wadannan boma-boman da nufin kashe sojojin kasar.

Labarin ya kara da cewa sojojin har'ila yau sun sami nasarar wargaza wuraren buyar yan ta'addan kimani 342 a duk fadin yankin. Sannan sun gano makamai da kayakin yaki masu yawa a wurare.

Banda haka an halaka yan ta'adda 27 a tsakanin wannan lokacin. 

Tun shekara ta 2014 kungiyoyin yan ta'adda suka bulla a yankin Sina na kasar Masar, sannan rayukan dukkan mutane, wadanda suka hada da jami'an tsaro da fararen hula ne suka salwanta a yankin daga wancan lokacin.