Gwamnatin Libya Ta Yi Gargadi Akan Yiyuwar Dawowar Da'esh
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34470-gwamnatin_libya_ta_yi_gargadi_akan_yiyuwar_dawowar_da'esh
Gwamnatin kasar ta Libya ta ce; Tare da cewa an kwato garin Sirte daga hannun Da'esh sai dai hakan baya nufin an murkushe kungiyar baki daya
(last modified 2018-12-18T03:55:16+00:00 )
Dec 18, 2018 03:55 UTC
  • Gwamnatin Libya Ta Yi Gargadi Akan Yiyuwar Dawowar Da'esh

Gwamnatin kasar ta Libya ta ce; Tare da cewa an kwato garin Sirte daga hannun Da'esh sai dai hakan baya nufin an murkushe kungiyar baki daya

Sanarwar gwamnatin wacce jaridar al-wasat ta buga ta ambaci cewa; Har yanzu da akwai gyauron kungiyar da suke jiran dama domin sake dawowa da karfinsu

Wannan sanarwar dai ta zo ne adaidai lokacin da ake bikin cika shekaru biyu da 'yanto garin Sirte daga hannun Da'esh.

A ranar 17 ga watan Disamba ne na 2016 shugaban gwamnatin hadin kan kasa Fayez al-Sarraj ya sanar da 'yanto garin na Sirte daga hannun Da'esh.

Kasar Libya tana fama da rashin tsaro tun faduwar gwamnatin Mu'ammar Khaddafi a 2011.