Najeriya Ta Nuna Damuwarta Dangane Da Ayyukan Kungiyar Amnesty Internatinal A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34475-najeriya_ta_nuna_damuwarta_dangane_da_ayyukan_kungiyar_amnesty_internatinal_a_kasar
Majiyar fadar shugaban kasa a tarayyar Najeriya ta nuna damuwarta da ayyukan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, don ayyukan nata suna shafar shirin gwamnati na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.
(last modified 2018-12-18T15:29:17+00:00 )
Dec 18, 2018 15:29 UTC
  • Najeriya Ta Nuna Damuwarta Dangane Da Ayyukan Kungiyar Amnesty Internatinal A Kasar

Majiyar fadar shugaban kasa a tarayyar Najeriya ta nuna damuwarta da ayyukan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, don ayyukan nata suna shafar shirin gwamnati na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar faransa ya nakalto fadar shugaban kasa tana fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa kungiyar Amnesty International tana wasu abubuwa wadanda suke kashe guiwar Jami'an tsaron kasar wadanda suke yaki da yan ta'adda na kungiyar Boko Haram. 

Kafin haka dai sojojin Najeriya sun zargi hukumar UNICEF mai kula da yara kanana ta Majalisar dinkin duniya da laifin horarda yan leken asirin kungiyar Boko Haram a birnin Maiduguri. 

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama suna zargin jami'an tsaron Najeriya ta take hakkin bil'adama a yakin da suke yi da kungiyar ta Boko Haram a kasar.