Jirgin Saman Daukar Kaya Ya Fadi A Kasar Congo Kinshasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34518-jirgin_saman_daukar_kaya_ya_fadi_a_kasar_congo_kinshasa
Kamfanin jiragen sama na kasar Congo Kinshasa ya bada labarin cewa jirgin kamfanin mai daukar kaya ya fadi a lokacinda yake dawowa birnin Kinshasa bayan ya kai kayakin zabe a garin Tshikapa kusa da kan iyakar kasar da kasar Angola a ranar Alhamis.
(last modified 2018-12-22T03:29:44+00:00 )
Dec 22, 2018 03:29 UTC
  • Jirgin Saman Daukar Kaya Ya Fadi A Kasar Congo Kinshasa

Kamfanin jiragen sama na kasar Congo Kinshasa ya bada labarin cewa jirgin kamfanin mai daukar kaya ya fadi a lokacinda yake dawowa birnin Kinshasa bayan ya kai kayakin zabe a garin Tshikapa kusa da kan iyakar kasar da kasar Angola a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran NAN na gwamnatin tarayyar Najeriya ya nakalto Jean De Dieu Karekezi wani jami'in kamfanin jiragen sama na Gomair mallakin gwamnatin kasar Congo Kinshasa yana fadar haka,

ya kuma kara da cewa jirgin ya bace a na'urar rada a ranar Alhamis amma sai a jiya jumma'a suka tabbatar da cewa ya fada. Jami'in bai bayyana yawan asarorin da aka yi na rayuka da dukiyoyi a wannan hatsarin ba. 

Gwamnatin kasar Congo ta bayyana cewa hukumar zaben kasar ce ta dauki hayan jirgin don isar da kayakin zabe zuwa garin tshikapa da ke kusa da kan iyakar da kasar Angola.

Sai kuma kakakin hukumar zaben kasar ta Congo CENI, ta bada sanarwan cewa jami'inda ya tafi tare da jirgin yana Tshikapa a lokacin da hatsarin ya auku.

Wannan hatsarin ya auku ne a dai-dai lokacinda tashe-tashen hankula, da kuma rashin kammala wasu shirye-shiryen zaben suka tilastawa hukumar zaben dage zaben na gobe Lahadi zuwa wata lahadi.