Macron Da Deby Sun Nuna Matukar Damuwa Kan Hare-Haren Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34545-macron_da_deby_sun_nuna_matukar_damuwa_kan_hare_haren_boko_haram
Shugabannin kasashen Faransa da na Chadi, sun nuna damuwa matuka dangane da yadda hare-haren kungiyar Boko Haram ke kara ta'azzara a yankin tafkin Chadi.
(last modified 2018-12-24T05:57:27+00:00 )
Dec 24, 2018 05:57 UTC
  • Macron Da Deby Sun Nuna Matukar Damuwa Kan Hare-Haren Boko Haram

Shugabannin kasashen Faransa da na Chadi, sun nuna damuwa matuka dangane da yadda hare-haren kungiyar Boko Haram ke kara ta'azzara a yankin tafkin Chadi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da suke ganawa a jiya a birnin Njamina na kasar Chadi, shugaban faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Chadi Idris Deby, sun tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi tsaroa  yankin tafkin Chadi.

Babban abin da tattaunawar shugabannin biyu tafi mayar da hankali a kansa shi ne barazanar kungiyar Boko Haram, da kuma karuwar ayyukanta na ta'addanci a kasashen yankin tafkin Chadi, da kuma yadda ya kamata a kara zage dantse domin tunkarar wannan barazana.

Macron ya ce kungiyar tarayyar turai za ta ware kudi har euro miliyan 55 domin wannan aiki, domin tabbatar da cewa an kakkabe hannun Boko haram tare da dawo da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Shugaban na Faransa ya isa kasar Chadi ne a jiya, domin ya yi bukukuwan kirsimati a sansanin sojin kasar Faransa da ke kasar ta Chadi, tare da sojojin kasarsa.