Sudan: Madugun Adawa Ya Yi Allawadai da Murkushe Masu Zanga-Zanga
Tsohon Firayi ministan kasar Sudan kuma madugun adawa a halin yanzu a kasar Sadikul Mahdi, ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da irin matakan da jami'an tsaron gwamnatin kasar suke dauka a kan masu zanga-zanga.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Sadikul Mahdi ya bayyana cewa, al'ummar kasa suna da hakkin su gudanar da zanga-zangar lumana, kuma manufar yin amfani da karfi da jami'an tsaro suka yi shi ne hargitsa lamarin, ta yadda za a haramta zanga-zangar baki daya.
Ya ce abin ban takaici ne yadda jami'an tsaron gwamnati za su yi amfani da kayan tsaro na kasa mallakin al'umma wajen kashe 'yan kasa, saboda suna kokawa kan tsadar rayuwa, a lokacin da abin da za su ci ke neman ya gagare su, saboda irin salon siyasar da gwamnatin kasar take bi wajen takura ma jama'a, alhali tsawon shekaru babu abin da ta tsinana musu, sai abin da ya kira surutu na fatar baki kawai.
Tun a cikin shekara ta 1989 ne dai Umar Hassan Albashir ya yi wa Sadikul Mahdi juyin mulki, inda ya dare kan shugabancin kasar da kakakin soji, inda har yanzu yake ci gaba da mulkin kasar.
Kotun duniya tana zargin Albashir da yin amfani da karfi wajen danne al'ummomin wasu yankuna na Sudan wadanda ba larabawa ba, tare da fifita larabawa a cikin dukkanin harkokin gwamnati, kamar yadda ake zarginsa da yin kisan kiyashi a kan bakaken fata wadanda ba larabawa a yankin Darfur.