Mahara Sun Kashe Mutane 17 A Jahar Zamfara
Dec 24, 2018 15:31 UTC
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato kakakin 'yan sanda na Jahar ta Zamfara Muhammad Shehu yana cewa; An Kashe mutane sha bakwai ne a wani hari da aka kai a garin Maradun da ke jahar
Muhammad Shehu ya kara da cewa; Tuni jami'an tsaro sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro, tare kuma da yin kira ga mutane yankin da su ba da hadin kai
Wani shaidar ganin ido a yankin na Muradun ya ce; Maharan sun zo ne akan babura, inda su ka yi ta harbin mutane a lokacin da suke guduwa
A cikin watannin bayan nan kai hare-hare sun tsananta a cikin jahar ta Zamfara da hakan ya tilastawa dubban mutane karkara yin hijira zuwa inda za su sami aminci.