Shugaban Kasar Sudan Ya Yi Alkawarin Kyautata Tattalin Arzikin Kasarsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34564-shugaban_kasar_sudan_ya_yi_alkawarin_kyautata_tattalin_arzikin_kasarsa
A maida martani na farko tun bayan fara zanga-zanga kan lalacewar tattalin arzikin kasar, shugaban kasar Sudan Umar Hassan al-bashir ya yi alkawarin kwatata tattalin arzikin kasar da kuma rayuwar mutane.
(last modified 2018-12-25T04:15:19+00:00 )
Dec 25, 2018 04:15 UTC
  • Shugaban Kasar Sudan Ya Yi Alkawarin Kyautata Tattalin Arzikin Kasarsa

A maida martani na farko tun bayan fara zanga-zanga kan lalacewar tattalin arzikin kasar, shugaban kasar Sudan Umar Hassan al-bashir ya yi alkawarin kwatata tattalin arzikin kasar da kuma rayuwar mutane.

Tashar talabijin ta "Al-hadith" ta nakalto shugaba Umar Hassan al-bashir yana fadar haka a jiya litinin da dare, a lokacinda yake ganawa da manya-manyan jami'an sojojin kasar a birnin Khartun. 

Shugaba Al-bashir ya yabawa jami'an tsaron kasar Sudan da kokarin da suka yi na tabbatar da cewa rikicin da ya taso baya-bayan nan bai yado ba. Ya kuma yi alkawarin gabatar da sauye-sauyen a harkokin bankuna da kuma wasu sassan tattalin arzikin kasar don samarwa mutanen kasar rayuwa mai mutunci. 

Banda haka shugaban hukumar yansandan ciki na kasar ta Sudan ya yi alkawarin murkushe dukkan wadanda ya kira masu tada hankali a kasar.

Kimani mako guda kenan mutane, musamman daliban jami'a a birnin Khartum da kuma wasu yankuna a kasar ta Sudan suka gudanar da zanga-zanga na yin allawadai da mummunan hali da tabarbarewar tattalin arziki wanda kasar ta fada ciki.

 Jami'an kasar Sudan sun bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane 8 suka rasa rayukansu a rikicin, sannan an rufe makarantu da jami'oi daga cikin har da Jami'an Khartun a babban birnin kasar. A wasu wurare kuma an kafa dokar hana fita.