Libya: Kungiyar Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A Birnin Tripoli
Kungiyar 'yan ta'addar ta fitar da wani bayani a jiya Talata da dare da a ciki ta bayyana cewa; ita ce ta kai hari akan ma'aikatar harkokin wajen kasar a birnin Tripoli
Da safiyar jiya Talata ne dai dai wasu mahara su 4 suka dumfari ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke birnin Tripoli, inda su ka tarwatsa kawukansu
Dukkanin maharan su uku sun halaka yayin da wasu mutane 9 su ka jikkata
Libya na fuskantar matsalar tsaro wacce ta samo asali tun 2011 da aka kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi ta hanyar tsoma bakin Amurka da kasashen turai
Bugu da kari har yanzu ana ci gaba da samun sabani a tsakanin bangarorin siyasar kasar da su ka kafa gwamnatoci biyu a cikin biranen Tubruk da kuma Tripoli. Gwamnatin hadin kan kasar da aka kafa a karkashin Fayez Suraj tana samun goyon bayan kasashen turai da su ka hada da Amurka, sai dai har yanzu ba ta shimfida ikonta a dukkanin fadin kasar ba.