Habasha: An Kama Jami'an Gwamnati 56 Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Dec 26, 2018 03:40 UTC
A jiya Talata ne gwamnatin kasar ta Habasha ta sanar da kame jami'ai 56 a karkashin fada da cin hanci da rashawa
Jami'an gwamnati da aka kama sun fito ne daga yankin Oromia da ke tsakiyar, suna fuskantar tuhumar salwantar da dukiyar gwamati
Hukumar da take fada da cin hanci da rashawa ta kasar na shirin kama wasu jami'an gwamnatin anan gaba, bisa zargin yi wa dukiyar kasa ta'annati
A cikin watan Nuwamba na wannan shekarar ma an kama wasu jami'an soja da aka zarga da aikata manyan laifuka
Pira ministan kasar ta Habasha, Abiye Ahmed ya yi alkawalin fada da cikin hanci da rashawa.