Fafatawa Tsakanin Yan Adawa Da Jami'an Tsaron Kasar Congo Brazavile
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34586-fafatawa_tsakanin_yan_adawa_da_jami'an_tsaron_kasar_congo_brazavile
Jami'an yansanda a kasar Democradiyyar Kongo sun yi amfani da hayakin mai sa hawaye don tarwatsa yan adawa masu zanga-zanga.
(last modified 2018-12-28T03:13:53+00:00 )
Dec 28, 2018 03:13 UTC
  • Fafatawa Tsakanin Yan Adawa Da Jami'an Tsaron Kasar Congo Brazavile

Jami'an yansanda a kasar Democradiyyar Kongo sun yi amfani da hayakin mai sa hawaye don tarwatsa yan adawa masu zanga-zanga.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a jiya Alhamis ne jami'an yansandan kasar suka kara da yan adawa masu zanga-zangar yin allawadai da dage zaben da hukumar zaben kasar ta yi, sannan musamman ware wasu garuruwa inda yan adawa suka da karfi, kan cewa ba za'a gudanar da zabe a cikinsu ba saboda abinda hukumar ta kira tsoron yaduwar cutar Ebola.

A ranar laraban da ta gabata ce hukumar zabe a kasar Kongo ta bada sanarwan cewa ba za'a gudanar da zabe a garuruwan Benny, daga gabacin kasar da kuma Yumbi daga yammacin kasar da kuma garin Butembo saboda tsoron yaduwar cutar Ebola. 

Wadannan yankunan ukku dai suna goyon bayan dan takarar adawa ne mai suna Emmanuel Ramazani Shadary ne, don haka hana zabe a yankunan zai bawa dan takara wanda shugaban kasa mai sauya Josept Kabila yake goyon bayan samun nasara a zaben. 

Tun shekara ta 2016 ne yakamata a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin kasar Kongo amma shugaban Josept Kabila yayi ta jan kafa har zuwa yanzu ba'a gudanar da zaben ba.