Kasar Congo Ta Kori Jakadan Tarayyar Turai
Jamhuriyar Demokraiyyar Congo ta kori jakadan Tarayyar Turai daga cikin kasar saboda abin da ta kira salon siyasar tarayyar akan kasar
Tashar talabijin din France 24 ta ba da labarin cewa kwanaki biyu gwabanin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisar dokoki da kananan hukumomi, ministan harkokin wjaen kasar Leonard She Okitundu ya kira yi tarayyar turai da ta janye jakadanta Bart Very a cikin sa'oi 48.
Kasar Congon ta dauki matakin ne a matsayin mayar da martani akan takunkumin da tarayyar turai din ta kakabawa wasu 'yan kasar ta Congo da su ka hada da dan takarar shugaban kasar, Ramadany SHadary, wanda yake samun goyon bayan Josheph Kabila.
Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi ne akan wasu mutane 13 da su ka hada da Shadary bisa zarginsu da yi wa harkokin zabe kafar anulu da kuma take hakkin dan'adam
A gobe Asabar ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa, na 'yan majalisar dokoki da kuma na gundumomin.