'Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an 'Yan Sanda 10 A Burkina Faso
'Yan ta'adda masu da'awar jihadi sun kashe jami'an 'yan sanda 10 a kasar Burkina Faso.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da rundunar 'yan sandan kasar Brkina Faso ta fitar ta tabbatar da mutuwar jami'anta su 10, a lokacin da suka nufi wata makaranta a wani kauye da ke arewa maso yammacin kasar a kusa da iyaka da kasar mali, bayan da 'yan ta'adda suka mamaye makarantar.
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, 'yan ta'adda sun yin amfani da manyan makamai da suka hada da manyan bindigogi a lokacin da suke yin musayar wuta da 'yan dandan.
Kasar Burkina Faso na fuskantar barazanar 'yan ta'adda masu tsatsauran ra'ayin akidar wahabiyanci da suke da alaka da kungiyar alkaida da ke da'awar jihadi, wadanda suke shigowa cikin kasar daga kasar Mali domin kaddamar da hare-hare.
Daga shekara ta 2015 ya zuwa yanzu, hare-haren ta'addancin wadanda kungiyoyi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 250 a kasar Burkina faso, da suka hada da jami'an tsaro da kuma fararen hula.