An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Congo
Da safiyar yau ne aka bude rumfunan zabe a jamhuriyar dimukradiyyar Congo, domin gudanar da zaben shugaban kasa a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran faransa ya bayar da rahoton cewa, jami'an hukumar zaben kasar ne suka fara kada kuri'unsu, kamar yadda kuma sauran jama'ar gari suka shiga cikin layuka a mazabu domin kada kuri'unsu.
Ana gudanar da zaben na yau ne dai bayan daga lokacin gudanar da shi har sau uku, inda za a zabi shugaban kasa wanda zai maye gurbin shugaba Joseph Kabila, inda 'yan takara uku za su fafata da juna.
Ana sa ran za a sanar da sakamakon zaben daga nan zuwa ranar 15 ga watan Disamba na shekara ta 2019 mai kamawa, kamar yadda kuma zababben shugaban kasar zai yi rantsuwar kama aiki a ranar 18 ga watan na Janairu.