Iritrea ta Rufe Wata Mashiga Da Ke Kan Iyakar Kasar Da Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34612-iritrea_ta_rufe_wata_mashiga_da_ke_kan_iyakar_kasar_da_habasha
Gwamnatin kasar Iritrea ta rufe daya daga cikin manyan hanyoyin da suke kan iyakar kasar da kuma kasar Habasha, bayan bude mashigar watanni uku da suka gabata.
(last modified 2018-12-30T03:31:43+00:00 )
Dec 30, 2018 03:31 UTC
  • Iritrea ta Rufe Wata Mashiga Da Ke Kan Iyakar Kasar Da Habasha

Gwamnatin kasar Iritrea ta rufe daya daga cikin manyan hanyoyin da suke kan iyakar kasar da kuma kasar Habasha, bayan bude mashigar watanni uku da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta Iritrea ta rufe mashigar Zalambasa da ke kan iyakar kasar da Habasha, ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.

An bude mashigar Zalambasa nea  cikin watan Satumban da ya gabata, biyo bayan yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, tare da dawo da alaka a tsakaninsu.

Wasu na danganta wannan mataki da Irirea ta dauka da yadda dubban 'yan kasar Habasha suke yin amfani da wannan mashigar wajen shiga cikin kasar ta Iritrea, domin isa gabar ruwa.