Shugaban Kasar Mauritaniya Zai Ziyarci Kasar Siriya
Wata majiya a fadar shugaban kasar Mauritaniya ta bada labarin cewa shugaban kasar Mohammad Wuld Abdul Aziz, zai kai ziyarar aiki kasar Siriya a tsakiyar wannan watan da muke ciki.
Majiyar muryar JMI ta nakalto majiyar fadar shugaban kasar tana bayyana haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa shugaban zai yi kwanaki biyu a kasar Siriya a lokacin ziyarar.
Shugaban kasar Sudan ne ya fara bude kofar ziyarar shugabannin kasashen Larabawa zuwa kasar Siriya a shekarar da ta gabata, daga nan ne da dama daga cikin wadannan kasashen suka fara shirye-shiryen sake bude ofishin jakadansu a birnin Damuscus.
Shugaban kasar Mauritania dai shi ne zai zama shugaba kasa daga cikin kasashen Larabawa da zai ziyarci kasar Siriya tun bayan shan kayen da kasar Saudiya da kawayenta suka sha a tsawon shekaru kimani 7 na kifar da gwamnatin shugaban Bashar Al-asad.
A cikin watan Maris na shekara ta 2011 gwamnatin kasar Saudiya da kawayenta da kasashen yankin da kuma kasashen yamma suka shigo da kungiyoyin yan ta'adda daban -daban kasar Siriya da nufin kifar da gwamnatin kasar.