Senegal: An Soke 'Yan Takarar Shugaban Kasa 22 Na "Yan Adawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34659-senegal_an_soke_'yan_takarar_shugaban_kasa_22_na_yan_adawa
Majalisar Tsarin mulkin kasar Senegal ce ta soke sunayen mutane 22 daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyun adawa 25
(last modified 2019-01-03T15:34:57+00:00 )
Jan 03, 2019 15:34 UTC
  • Senegal: An Soke 'Yan Takarar Shugaban Kasa 22 Na

Majalisar Tsarin mulkin kasar Senegal ce ta soke sunayen mutane 22 daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyun adawa 25

Tashar talabijin din France 24 ta ba da labarin cewa; Majalisar tsarin mulkin kasar ta Senegal wacce ita ce cibiya ta karshe ta fuskar shari'a da doka, ta soke cancantar 'yan takarar shugabancin kasar ne a jiya Laraba

Bugu da kari, majalisar tsarin mulkin ta ce; Mutanen sun kasa samun sa hannun mutane 52,000 kamar yadda doka ta tanada domin samun damar yin takara

Majalisar ta kuma bai wa 'yan adawar sa'o'i 48 da su zo da rattaba hannun mutanen.

Sai dai 'yan hamayyar sun nuna kin amincewarsu da matakin na Majalisar tsarin mulki

Za a gudanar da zaben shugaban kasar Senegal ne a ranar 24 ga wata Fabrairu mai zuwa