Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Mummunan Hari A Kasar Mali
Jan 03, 2019 15:39 UTC
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce; Rundunar MDD ta tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Mali MINUSMA ta fitar da bayani a jiya laraba da a ciki ta yi Allah wadai da harin da aka kai a garin Mopti wanda ya ci rayukan mutane
A kalla mutane 37 mafi yawancinsu mata da kananan yara ne aka kashe a yayin harin da aka kai da safiyar ranar Talata
Bayanin ya ci gaba da cewa; Maharan da ba a tantance su ba sun kunna wuta a gidanen mutanen garin na Mopti wanda ya haddasa barnar dukiya da rayuka
Tsakiyar kasar Mali tana fuskantar rashin tsaro tun 2016 saboda fadace-fadace masu alaka da kabilanci. Fiye da mutane 500 ne aka kashe a cikin yankin a shekarar 2018 da ta wuce