Za A Dage Sanar Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Hukumar zaben kasar Demokradiyyar Congo ce ta sanar da yiyuwar dage lokacin sanar da sakamakon farko na zaben
Kakakin hukumar zaben kasar Jean Pierre Kalamba ya ce; A bisa yadda aka tsara a baya za a fara sanar da sakamakon farko na zaben shugaban kasar ne a ranar Lahadi 6 ga watan nan na Janairu sai dai abu ne mai yiyuwa a dage lokacin.
Kakakin hukumar zaben ya kara da cewa; A halin yanzu ana ci gaba da kidaya kuri'un da aka kada, kuma za a rika sanar da su sannu a hankali
Shi kuwa shugaban tawagar masu sa ido a zaben na kasar Congo wanda ya wakilci tarayyar Afirka Sioncounda Traore ya soki yadda aka gudanar da zaben yana mai cewa ba a gudanar da shi cikin tsari ba, sannan kuma ya bukaci ganin cewa sakamakon da za a sanar ya yi daidai da kuri'un da mutane su ka kada
A bisa yadda aka tsara za a sanar da zabe na karshe ne a ranar 15 ga watan Janairu da ake ciki
A ranar 30 ga watan Disamba da ya wuce ne aka gudanar da Zaben shugaban kasar Demokradiyyar Congo.
Wannan ne dai shi ne karon farko da za sami sauyin gwamnati a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a cikin ruwan sanyi tun samun 'yancin kasar daga 'yan mulkin mallakar Belgium a 1960