Ana Ci Gaba Da Zanga -Zanga A Kasar Sudan
Jami'an tsaron kasar Sudan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga- Zanga a garin Port Sudan a jiya Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa masu zanga-zanga wadanda yawansu ya kai mutane dubu 200 su tunkari ofishin jam'iyya mai mulkin kasar Sudan da nufin mika wata takarda wacce suka rubuta bukatunsu a ciki, amma jami'an tsaron kasar suka yi amfani da hayaki mai sa hawaje don tarwatsasu.
Banda Port Sudan dai an yi irin wannan zanga-zangar a wasu yankunana a kasar ta Sudan a cikin yan kwanakin da suka gabata, kuma jami'an tsaro a wadannan yankunan sun yi amfani da karfi wajen tarwatsasu.
muatanen kasar Sudan dai suna bukatar shugaban kasar Umar Hassan Albashir ya sauka daga mukaminsa, sannan a shirya zabe mai inganci a nan gaba a kasar.
An fara zanga-zanag a kasar Sudan ne tun ranar 19 ga watan Decemba na shekarar da ta gabata bayan da kayakin bukatun yau da kullum wadanda suka hada da biredi suka yi tashin goron zabe a duk fadin kasar.
A bayanan da aka ji daga shugaba Umar Hassan Albashir na baya-bayan nan dai suna cewa yana tunanin karawa ma'aikata albashi.