Karfin Makamai Masu Linzami Na Palasdinawa Ya Karu A Shekara Ta 2018
Sojojin HKI sun bada sanarwan cewa a cikin shekarar da ta shude karfin makamai masu Linzami ko kuma Rocket na Palasawa a yankin Gazza ya karu har sau 10 idan an kwatanta da shekaru ukku da suka gabata. Banda haka karfin garkuwan makamai masu linzami na HKI bai kai yadda ake zata ba, don ta kasa hana mafi yawan makaman roccket na gungiyar Hamas faduwa a kan yankunan da yahudawa suke zaune a haramtacciyar kasar.
Dangane da irin ci gaban da al'ummar Palasdinu musamman wadanda suke yankin Gaza suka sami na ci gaba da gina makamai masum linzami a yankin nasu da kansu ba tare da sun shigo da su daga waje ba, yana daga cikin manya-manyan ci gaban da Palasdinawa suka samu a cikinn shirara da 2018 da ta gabata.
Masana suna ganin da karfin wadannan makamai ne kungiyar Hamasa da kuma sauran kungiyoyin Palasdinawa suka sami nasara kan sojojin HKI, inda makamai masu linzami ko kuma Rocket wadanda dakarun izzuddin Qassam suke yi ta cilla kan matsugunan yahudawan sahyoniyya a yankunan Palasdinu da aka mamaye sun tilastawa HKI amince da sharuddan Palasdiwan kafin a dakatar da budewa juna wuta.
Dangane da wannan labarin Jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta rubuta a shafinta irin nasarar da mayakan kungiyar Hamas suka sami a fafatawan baya-bayan nan ya nuna irin ci gaban da Hamsa ta sami da kuma nasarar da ta samu a kan sojojin yahudawa wadanda suka kada hana daruruwan makamai masu linzami wadanda Hamas take cilliwa daga yankin Gaza zuwa matsugunan yahudawa.
Al-Ahram ta kara da cewa wannan ci gaban ya tsorata HKI har sai da ya kai ga Ministan yakin haramtacciyar kasar Liverman ya ajiye mukaminsa sannan yahudawan suka shelanta gudanar da zabe tun kafin lokacinsa ya yi, wanda yake nuna cewa ana iya samun sauyin gwamnati a haramtacciyar kasar.
Sauye-sauyen da aka samu a gwagwarmayan al-ummar Palasdinu da HKI ya kara karfi wa kawancen masu gwagwarmaya da yan ta'adda da kuma HKI a yankin gabas ta tsakiya. Wannan karfin da bangaren masu gwagwarmaya suka samu a dukkan bangarori ya tabbatar da cewa shirin shugaban kasar Amurka na "Sulhun Karbi " ba zai kai labari ba. Kuma dukkan abinda suka kulla na sharri a yankin gabas ta tsakiya, musamman a kan al-ummar Palasdinu ba zai sami nasara ba.
Kafin haka dai wani masanin harkokin yaki na HKI mai suna Muti Shefer ya bayyana cewa garkuwan makamai masu linzami wadanda HKI tana ganin wata garkuwa ce mai amince, ya bayyana a fili kan cewa wata yaudare ce kawai, don gashi ta kasa kare yahudawan sahyoniyya daga kananan rokoki wadanda mayakan Palsdinawa suke cillawa daga yankin Gazza , wannan duk tare da kofar ragon da ake wa yankinn fiye da shekaru 10 da suka gabata.
A rahotonta na shekara-shekara, sojojin HKI sun bayyana cewa a cikin shekaru ukku da suka gabata rokoki daga yankin Gaza da suka fada cikin kudancin Paladinu da aka mamaye bai kai 100 ba, amma a shekara ta 2018 kadai fiye da rokoki 1000 guda ne suka fada a wadannan yankuna wadanda ya nuna irin ci gaban da Palasdinawa suka samu a cikin dan wannan lokacin.
Daga karshe yahoton ya bayyana cewa daga cikin rokoki kimani 1000 da aka cillasu kan yahudawan daga yanzin Gaza, guda 100 ne kacal garkuwan makaman linzamin da aka girka a duk fadin yankunan suka kakkabo.