Tarayyar Afrika Ta Kirayi Gwamnatin Congo Da Ta Mutunta Sakamakon Zabuka
Kungiyar tarayyar Afrika ta bukaci gwamnatin jamhuriyar dimukradiyyar Congo da ta mutunta sakamakon zabukan da aka gudanara kasar.
Kamfanin dilalncin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a lokaci da yake ganawa da shugaban tawagar kungiyar tarayyar Afrika masu sanya ido kan zaben Congo a yau a birnin Adddis Ababa na kasar Habasha, shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar Afrika Musa Faqi Muhammad ya bayyana cewa, girmama sakamakon zaben ya zama wajibi a kan gwamnatin Congo da sauran bangarori.
A nata bangaren babban majalisar Katolika ta kasar Congo ta bayyana cewa, ta san wanda ya lashe zaben shugaban kasar, kuma tana jiran gwamnati ta yi adalci ta amince da hakan.
A can birnin Geneva na kasar Switzerland kuwa, mai magana da yawun kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, ci gaba da tsorata 'yan jarida da masu fafutuka da 'yan adawar siyasa da gwamnatrin kasar Congo ke yi, bayan gudanar da zabukan 30 ga watan Disamban da ya gabata, abu ne da ke sanya ayar tambaya kan manufar hakan, musamman a wannan lokaci da ake jiran sanar da sakamakon zaben.