Rikicin Kabilanci ya Lashe Rayukan Mutane 46 A Burkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34681-rikicin_kabilanci_ya_lashe_rayukan_mutane_46_a_burkina_faso
Wani rikicin kabilanci da ya kunno kai a kasar Burkina Fasoa cikin 'yan kwanakin nan ya lashe rayukan mutane akalla 46.
(last modified 2019-01-05T11:47:46+00:00 )
Jan 05, 2019 11:47 UTC
  • Rikicin Kabilanci ya Lashe Rayukan Mutane 46 A Burkina Faso

Wani rikicin kabilanci da ya kunno kai a kasar Burkina Fasoa cikin 'yan kwanakin nan ya lashe rayukan mutane akalla 46.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, jami'an 'yan sandan kasar Burkina Faso sun sanar a jiya  abirnin Wagadugu cewa, tun daga ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata aka fara wani rikicin kabilanci, wanda ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 46 a kasar.

Bayanin ya ce wasu mutane dauke da makamai suka fara kaddamar da farmaki a kan mutanen kauyen Yirgou, inda suka kashe mutane bakawai, daga nan kuma sai mutanen kauyen suka yi inda su ma suka kai wani hari a kan wasu kauyuka na fulani, inda suka kashe mutane kimanin 38, kuma har yanzu ana ci gaba da zaman dardar a yankunan.

Kasar Burkina faso ta fara fuskantar irin wadannan matsalolin ne tun bayan da 'yan ta'adda masu da'awar jihadi suka fara saka kafarsua  cikin kasar daga kasar Mali mai makwabtaka da ita, yanzu haka dai an tura jami'an tsaro zuwa yanzkunan da ake fama da rikicin, domin tabbatar da tsaro da kuma dawo da doka da oda.