Najeriya: Jami'an Tsaro Sun Yi Awon gaba Da Ma'aikatan Jaridar Daily Trust
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, a jiya Lahadi jami'an tsaro sun yi awon gaba da ma'akatanta guda biyu a birnin Maiduguri na jahar Borno, sakamakon wani rahoto da jaridar ta bayar da ke da alaka da Boko Haram.
Jaridar ta ce sojoji dauke da makamai sun kai samame a ofishin nata, inda suka yi awon gaba da shugaban ofishin a jahar Bornon Usman Abubakar, sai kuma wani dan jarida ma;aikacin kamfanin Ibrahim Sawab, kamar yadda kuma suka kwashe kayan aiki da suka hada da kwamfutoci da sauran kayan aiki da ke wurin.
Baya ga haka kuma jaridar ta kara da cewa, a jiya ma jami'an sojin sun kai wani samamen a ofisoshin jaridar da ke Abuja da kuma Lagos, inda suka kwashe kwamfutoci da wasu kayan aiki, kamar yadda kuma umarci ma'aikata da su fice daga wuraren.
Jaridar Daily Trust ta buga wani labari da ke cewa sojojin suna shirin kai farmaki kan mayakan Boko Haram da nufin sake kwace garin Baga na jahar Borno, inda a kwanakin baya jaridar ta buga cewa 'yan Boko haram sun kwace iko da garin, yayin da sojoji suka karyata hakan.