Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Kasar Gabon
Wasu rahotanni sun bayyana cewa sojoji a kasar Gabon sun kwace mulki daga hannun shugaban kasar Ali Bongo
Kamfanin dillancin labaran NAN na tarayyar Najeriya ya nakalto tashar "Radio France International" tana cewa wani soja mai suna Lieutenant Kelly Ondo Obiang ya shiga gidan radiyon kasar inda ya karanta wani jawabi a madadin sojojin kasar.
A cikin jawabin nasa Lieutenant Kelly Ondo Obiang ya yi watsi da jawabin da shugaban kasar Ali Bongo yayi na sabon shekara daga inda yake jinya a kasar Morocco.
Labarin ya kara da cewa sojojin zasu kafa komitin gudanarwa don karbar harkokin tafiyar da kasar kafin su san abinda zasu yi a nan gaba.
A halin yanzu dai sojojin sun kwace iko da manya-manyan hanyaoyin shiga kasar wadanda suka hada da babban tashar jiragen sama na Brazaville.
Shugaba Bongo dai yana wajen kasar Gabon tun watan Octoban shekarar da ta gabata, inda aka yi masa aikin tiyata a birnin Riyard na kasar Saudia sannan daga baya ya koma kasar Morocco inda a halin yanzu yake jinya.