An Kame Sojijin Da Su Ka Shirya Juyin Mulki A Kasar Gabon
Majiyar gwamnatin kasar Gabon ta ce; Al'amurra suna a karkashin gwamnati kuma tuni an kama wadanda su ka shirya juyin mulkin
Rahotanni sun ce tuni kwanciyar hankali ta dawo kan mafi yawancin titunan birnin libreville. An girke sojoji da 'yan sanda masu yawan gaske akan titunan baban birnin, yayin da jirage masu saukar angulu suke shawagi a sama
Wasu sojojin kasar ta Gabon ne su ka kai hari akan gidan Rediyon kasar inda su ka watsa sanarwar kafa majalisar gyaran kasa
Sojojin sun kuma bayyana cewa; jawabin karshe da shugaban kasar Ali Bango ya yi ya tabbatar da cewa ba zai iya tafiyar da al'amurran sha'anin mulki ba
Tun a cikin watan Oktoba na 2018 ne dai Ali Bongo da ya halarci taron tattalin arziki a kasar Saudiyya, ya kwanta a asibiti saboda rashin lafiya da yake fama da ita
A cikin kwanaki kadan da su ka gabata ne aka nuna hoton bidiyo na shugaban kasar ta Gabo wanda yake kwance a asibitin kasar Moroko, inda ya yi wa al'ummar kasar jawabi
A gefe daya kungiyar tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba
Shugaban cibiyar tarayyar Afirka Musa Faki ne ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa;Tarayyar Afirka ba ta yarda da duk wani kokarin sauya gwamnati wanda ya sabawa tsarin mulki ba