Bunkasa Harkar Adana Kayan Tarihi A Mauritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34724-bunkasa_harkar_adana_kayan_tarihi_a_mauritaniya
Dakin karatu na birnin Walata a kasar Mauritania ya bude wani baje kolin nuna tafsiran kur’ani mai tsarki guda 2500 da aka rubuta da hannu tun daruruwan shekaru.
(last modified 2019-01-08T09:00:59+00:00 )
Jan 08, 2019 09:00 UTC
  • Bunkasa Harkar Adana Kayan Tarihi A Mauritaniya

Dakin karatu na birnin Walata a kasar Mauritania ya bude wani baje kolin nuna tafsiran kur’ani mai tsarki guda 2500 da aka rubuta da hannu tun daruruwan shekaru.

Shafin yada labarai na Alarabi Jadid ya habarta cewa, wannan dakin karatu da ke a garin tarihi na Walata mai tazarar kilo mita 1300 daga kudu maso gabashin birnin Nuwakshot, yana daga cikin dakunan karatu masu matukar muhimmanci a halin yanzu a nahiyar Afrika baki daya.

Rahoton yace tafsiran kur’ani da ke cikin wurin mafi yawa an rubuta su ne tun a cikin karni na biyar hijira kamariya, fiye da shekaru dari tara da suka gabata.

An gina wannan dakin karatu nea cikin shekarar 1990 tare da taimakon masu bincike na kasar Spain, inda aka harhadalittafai masu kima a cikinsa, kuma a halin yanzu, wani bangarensa ya zama wajen ajiye muhimman kayan tarihin musulunci.

Haka nan kuma yanzu wurin ya zama wurin da masu yawon bude ido da kuma masu bincike suke ziyarta a kowace rana.

Manufar baje kolin dai ita ce nuna daddun abubuwa na tarihi da kasar ta Mauritaniya take da su, da kuam kara jawo hankulan masu yawon bude domin ganewa idanunsu.