An Kawo Karshen Gasar Kur’ani ta Kasa A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34726-an_kawo_karshen_gasar_kur’ani_ta_kasa_a_najeriya
Ann kammala gasar kur’ani ta kasa da aka gudanar a tarayyar Najeriya karo na 33.
(last modified 2019-01-08T09:11:12+00:00 )
Jan 08, 2019 09:11 UTC
  • An Kawo Karshen Gasar Kur’ani ta Kasa A Najeriya

Ann kammala gasar kur’ani ta kasa da aka gudanar a tarayyar Najeriya karo na 33.

Jaridar Independent ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, an kammala gasar a garin Gombe, tare da halartar jami’an gwamnati da kuma malamai.

Muhammad Yalwa shugaban kwamitin gasar ya bayyana cewa, mutane 344 ne suka halarci gasar daga jahohi 35 na kasar.

A wannan karon gasar ta gudana a bangarori daban-daban, daga ciki kuwa har da tarjamar ayoyin kur’ani bayan karanta su, inda Zainab Muhammad Paris daga Adamawa ta zo ta daya a bangaren mata, sai kuma Tijani Goni Danbaba daga Yobe ya zo na daya a bangaren maza.

Kowanne daga cikinsu ya samu kyautar kudi Naira dubu 500, kamar yadda kuma za su wakilci Najeriya a gasar kur’ani ta Saudiyya da Kuwait.