Jam'iyyar Da Take Mulki A Congo Tana Shakku Kan Sakamakon Zabe
Jami'yyar mai mulki a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo " Common Front For Congo" ta ce tana da hakkin daukaka kara akan sakamakon zabe na farko da aka fitar
Kakakin jam'iyyar mai mulki a kasar, Lambert Mende ya ce; Suna da hakkin daukar matakan sharia akan sakamakon farko na zaben shugaban kasar da hukumar zabe ta sanar
Jam'iyyar mai mulki ta tsayar da Emmanuel Ramazani Shadary ne a matsayin dan takararta da zai gaji shugaba Joseph Kabila idan ya ci zabe.
A yau alhamis ne hukumar zaben kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da cewa; dan takarar jam'iyyar hamayya, Felix Tshisekedi ne ya lashe zaben shugaban kasar
An gudanar da zaben shugaban kasar ne ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar 2018 da ta shude.
Wannan zai zama shi ne karon farko a tarihin kasar da farar hula zai karbi mulki daga farar hula ta hanyar zabe.
Shugaba Joseph Kabila ya hau kan karagar mulkin kasar ne tun bayan kashe mahaifinsa Laurence Kabila a 2001