An Kashe Mutane 8 A Rikicin Bayan Zaben Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34769-an_kashe_mutane_8_a_rikicin_bayan_zaben_kasar_jamhuriyar_demokradiyyar_congo
Majiyar 'yan sandan kasar ta Jamhuriyar Demokraidyyar Congo ta bayyana cewa; Rikicin bayan zabe ya ci rayukan mutane 8 a yammacin kasar
(last modified 2019-01-12T03:12:59+00:00 )
Jan 12, 2019 03:12 UTC
  • An Kashe Mutane 8 A Rikicin Bayan Zaben Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Majiyar 'yan sandan kasar ta Jamhuriyar Demokraidyyar Congo ta bayyana cewa; Rikicin bayan zabe ya ci rayukan mutane 8 a yammacin kasar

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto majiyar 'yan sandan na cewa; An kashe mutane 8 din ne a Kikwit da yake yammacin kasar

Majiyar ta kuma ci gaba da cewa; Wasu 'yan sanda 17 sun jikkata a sanadiyyar bata-kashi da masu Zanga-zanga

An gudanar da zaben shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ne a ranar 30 ga watan Disamba na 2018.

Sakamakon zaben ya bayyana Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben

Wannan shi ne karon farko da farar hula zai mika wa farar hula mulki a tsawon tarihin kasar tun daga samun 'yanci 1960

Joseph Kabila ya hau karagar mulki ne a 2001 bayan kashe mahaifinsa Laurence Kabila.