An Nada Sabon Firayi Minista A Kasar Gabon
Jan 12, 2019 09:44 UTC
Shugaban kasar Gabon ya nada sabon firayi ministan kasar, bayan sauke firayi ministan kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ofishin shugaban kasar Gabon ya sanar da sauke firayi ministan kasar Emmanuel Issoze Ngondet daga kan mukaminsa, tare da nada Julien Nkoghe Bekalé a madadinsa.
Shugaban kasar ta Gabon ya nada tsohon firayi ministan kasar Emmanuel Issoze Ngondet a matsayin mai ba shi shawara.
A cikin kwanakin da suka gabata ne dai wasu sojoji suka yi yunkurin juyin juyin mulki a kasar ta Gabon wanda bai yi nasara ba.