Najeriya: An Kasa Cimma matsaya Tsakanin ASUU Da Gwamnati
Kungiyar malaman jami'oi a Najeriya ASUU ta ce har yanzu ba a samu wata matsaya takaninsu da gwamnati ba.
A cikin rahoton da jaridar Premium Times ta bayar, ta bayyana cewa kungiyar ta ASUU ta ce har yanzu babu wata matsaya da aka cimmawa tsakaninsu da gwamnati dangane da bukatun da suka gabatar, a kan haka za su gaba da yajin aiki har sai baba-ta-gani.
Wasu bayanai sun ce gwamnati ta fitar da Naira biliyan 15.4 domin warware wasu daga cikin bukatun na ASUU, amma kungiyar ta ce abin da take bukata shi ne Naira biliyan 220 daga cikin naira Trilion 1.1. da suke bin gwamnati bashi.
ASUU ta zargi gwamnati da kasa aiwatar da yarjejeniyar da suka cimmawa a lokutan baya kan yadda za a biya su kudadensu, wanda hakan ya sanya kungiyar shiga yajin aiki tun daga ranar 4 ga watan Nuwamban 2018 da ta gabata.