"Yan Gudun Hijira Daga Najeriya Suna kwarara Zuwa Kasar Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34843-yan_gudun_hijira_daga_najeriya_suna_kwarara_zuwa_kasar_chadi
Gwamnatin kasar Chadi ta sanar da cewa 'Yan gudun hijira 7000 ne daga Najeriya su ka shiga cikin kasar
(last modified 2019-01-17T15:55:35+00:00 )
Jan 17, 2019 15:55 UTC

Gwamnatin kasar Chadi ta sanar da cewa 'Yan gudun hijira 7000 ne daga Najeriya su ka shiga cikin kasar

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato ma'aikatar tsaron kasar ta Chadi tana fada a yau alhamis cewa; A dalilin harin bayan nan da kungiyar boko haram ta kai a Najeriya, 'yan gudun hijira dubu bakwai sun kwarara zuwa gundumar Lac da ke kasar Chadi

Sanarwar ta kasar Chadi ta ci gaba da cewa; A halin yanzu ya fara rijistar mutanen

Daga fara hare-haren boko haram dubban 'yan Najeriya ne suka ketara iyaka cikin kasar Chadi domin samun mafaka daga tashe-tashen hankula

A halin yanzu da akwai 'yan gudun hijirar Najeriya 15,000 a kasar ta Chadi

Ma'aikatar tsaron kasar Chadi ta ci gaba da cewa; Duk da matsalolin tsaro da kasar take fuskanta, sai dai har yanzu kofarta a bude take domin karbar 'yan gudun hijira