Mali: Jiragen Yakin Faransa Sun Kashe 'Yan Ta'adda 15
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34854-mali_jiragen_yakin_faransa_sun_kashe_'yan_ta'adda_15
Rundunar sojin kasar faransa ta sanar da cewa, dakarun kasar sun samu nasarar halaka wasu 'yan ta'adda 15 a kasar mali.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jan 18, 2019 13:15 UTC
  • Mali: Jiragen Yakin Faransa Sun Kashe 'Yan Ta'adda 15

Rundunar sojin kasar faransa ta sanar da cewa, dakarun kasar sun samu nasarar halaka wasu 'yan ta'adda 15 a kasar mali.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar ad rahoton cewa, a cikin bayanin da rundunar sojin kasar ta faransa ta fitar a yau Juma'a, ta bayyana cewa jiragen yakin kasar ne suka kaddamar da hare-hare a kan 'yan bindigar,a  lokacin da suke shirin kai wasu munanan hare-haren ta'addanci a arewacin Mobti a cikin kasar mali, kuma sn kashe 15 daga cikinsu, wanda hakan ya rusa shirin nasu.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar ta faransa ya ce an yi amfani da jiragen yaki samfurin Atlantic 2 da kuma wasu jirage marassa matuki wajen kai harin, bayan gano shirin da 'yan ta'adda suke da shi, inda ya ce wannan babban abin farin ciki ne gare su, kuma za su kara daura damara tare da sojojin Mali domin ganin bayan 'yan ta'adda da suke barazana ga harkar tsaron kasar da ma kasashe makwabtan mali.

Bayanin ya kara da cewa, a farkon wanann watan na Janairu, sojojin Faransa tare da na gwamnatin mali, sun kaddamar da wani farmakia  kan wani sansanin 'yan bindiga a yankin Sirma, inda suka fatattake su, kuma suka kwashe tarin makamai da 'yan bindigar suka bari.