'Yan Ci-Rani Fiye Da 100 Sun Nutse A Tekun Mediterania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34871-'yan_ci_rani_fiye_da_100_sun_nutse_a_tekun_mediterania
Wani jirgin ruwa mai dauke da 'yan ci rani 120 da ke kan hanyar Libya zuwa Italiya ya nutse a tekun mediterania
(last modified 2019-01-20T03:00:24+00:00 )
Jan 20, 2019 03:00 UTC
  • 'Yan Ci-Rani Fiye Da 100 Sun Nutse A Tekun Mediterania

Wani jirgin ruwa mai dauke da 'yan ci rani 120 da ke kan hanyar Libya zuwa Italiya ya nutse a tekun mediterania

kamfanin dillancin labarun Italiya "Ansa' ya ba da labarin cewa; 'yan ci rani 117 sun rasa rayukansu

Jirgin ruwan ya nutse ne a ranar Alhamis ne da marece bayan sa'oi 11 ta barinsa kasar Libya

Mutane uku ne kadai da su ka fito daga kasashen Najeriya, Gambia, da Cote De voire aka iya cetowa a tsakanin su 120.

A bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya a cikin shekaru biyar na bayan nan mutane fiye da 30,000 ne 'yan ci-rani su ka mutu a cikin ruwa akan hanyarsu ta zuwa kasashen turai.

A shekarar 2018 da ta shude, mutane 2000 suka nutse a cikin tekun mediterania kadai.